An gurfanar da wanda ya kashe matar aure da diyarta a gaban Kotun Birnin kebbi, ya amsa laifinsa a gaban Alkali


Rundunar yansandan jihar Kebbi ta gurfanar da Idris Abubakar dan shekara 25 a gaban babban Kotun Majistare da ke Birnin kebbi ranar Alhamis 21 ga watan Aprilu 2022, bayan ya kashe wata matar aure Sadiya Idris tare da diyarta Khadijat mai shekara 4 da haihuwa ranar 11 ga watan Aprilu 2022. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.

An fara sauraron shari'ar Idris da karfe 3:38 na rana, bayan mai gabatar da kara na yansanda Safeto Jibrin Abba ya gabatar da kara da ake yi wa Idris Abubakar bayan ya karanta takardar shigar da kara a gaban Kotu.

Yansanda sun gurfanar da Idris ne bisa tuhuma guda biyu da suka hada da kutse cikin gidan mutane karkashin sashe na 336 na dokokin Penal code na jihar Kebbi da kuma aikata kisan kai karkashin sashe na 191 na dokokin Penal code na jihar Kebbi.

KARANTADa duminsa: An kama wanda ya kashe matar aure tare da diyarta a garin Birnin kebbi (Hotuna da Bidiyo)

Alkalin Kotu ya tambayi Idris ko ya fahimci kara da aka karanta masa na tuhumarsa da ake yi a gaban Kotu, Idris ya gaya wa Kotu cewa ya fahimta.

Alkali ya tambaye Idris cewa gaskiya ne ko akasin haka bisa tuhuma da yansanda suke yi masa a gaban Kotu.

Idris ya ce " Ba zan bata wa Kotu lokaci ba. Abin da ake tuhuma da shi gaskiya ne na aikata".

Sakamakon haka mai gabatar da kara na yansanda Safeto Jibrin ya ce har yanzu yansanda suna gudanar da bincike kan lamarin.

KARANTAKebbi: Bayan kama wanda ya kashe matar aure da diyarta a Birnin kebbi, Kakakin hukumar yan sandan jihar Kebbi ya yi karin bayani yadda ta faru (Bidiyo)

Ya kuma nemi Kotu ta dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 19 ga watan Mayu 2022 domin ba yansanda damar ci gaba da bincike tare da samun shawara daga ofishin shari'a na Director Public Prosecution DPP na jihar Kebbi.

Daga karshe Kotu ta dage shari'ar har zuwa ranar 19 ga watan Mayu 2022. Kazalika Alkalin Kotun ya yi umarnin a tasa keyar Idris Abubakar zuwa Kurkuku har zuwa wannan ranar domin ci gaba da gudanar da shari'ar. 

KARANTAMijin matar da aka kashe a Birnin kebbi, Mahaifinta , Yayar ta sun yi wani roko mai ratsa jiki (Bidiyo)

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN