Alamomi 10 da za ka iya fara ji idan ka kamu da HIV

Cutar kanjamau cuta ce da ta dade tana lahani ga bil'adama da akasari kan kai ga mutuwa daga karshe.

Ga wasu alamomi guda 10 da zaka kiyaye idan har ka fara kamuwa da kanjamau ko HIV sune alamomin da zaka iya fara ji kafin lamari yayi nisa.

1. Yawan tashin zuciya
2  Yawan amai maras dalili
3  Zawo babu kakkautawa
4  Gajiya mai nauyi kuma ba tare da anyi wani aiki ba 
5  Ragewar nauyi ko rama mai tsanani
6  Yawan tari da rashin wadatar nufashi
7  Yawan zazzabi
8  Mura da sanyi mai radadi da yawan zufa da dare
9  Bayyanar kaluluwa a tsakanin cinyoyi a kasan mara
10  Bayyanar kuraje a baki,hanci,harshe ko tsakanin matse-matsi
Kasancewa kana da daya ko fiye da buyu daga cikin alamomi da aka zana a sama ba kenan yana nufin tabbas kana da kanjamauba,ko wace cuta tana tafe da nata alamu kuma alamun sukan yi kama.A yi kokari aje ayi gwajin HIV wadda kyautane.

Isyaku Garba - Birnin kebbi

Shafin mu na Facebook
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08087645001.
Don aiko Labari ko korafi ka rubuto SMS zuwa 08087645001 ba za mu amsa kira ba,amma za mu karanta kuma mu mayar da martani ta SMS kawai/
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN