Recent Posts

 • Kalli bidiyo da Sanatoci ke kira a tsige shugaba Buhari kan rikicin Dino Melaye

  By Isyaku Garba → April 27, 2018
  Sakamakon matsalar da Sanata Dino Melaye ya shiga tsakaninsa da yansanda da kuma yadda al'amurra suka jagule wa Sanatan. A yau wasu Sanatoci sun fara kira cewa a tsige shuga Buhari.

  Kalli bidiyo:

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
 • An yi wa sajen na yansanda koran kare daga aiki sakamakon kashe da acaba

  By Isyaku Garba →
  Hukumar yansada a jihar Ebonyi ta kori wani jami'in dansanda mai mukamin sajen mai suna  Onyebuchi Nweke bayan ya harbe wani dan acaba mai suna Ejika har lahira domin ya ki ya ba shi cin hanci na N50 a Abakaliki na jihar ta Ebonyi.

  Lamarin ya faru a kan hanyar Water works da ke Abakaliki ranar Laraba 25 ga watan Afrilu.

  Kakakin hukumar yansanda na jihar Loveth Odah ya ce an kama dansandan kuma an same shi da laifin aikata kisa da gangan a tsarin hukuncin yansanda na Orderly room, sakamakon haka aka yi masa koran kare daga aikin dansanda .

  Kakakin ya ce bayan haka hukumar za ta gurfanar da korarren dansandan a gaban Kotu bisa zargin kisan kai da gangan.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
 • Yadda akwatin gawa ya ki shiga kabari, amma sojoji sun tilasta ya shiga - Hotuna

  By Isyaku Garba →
  Wani abin al'ajabi ya faru a kasar Zambia bayan wani akwatin gawa ya fara tafiyya da kansa  ba tare da an dauke shi ba, wai yana neman wani Maye mai suna Kikondo a gundumar Kaoma.

  Wannan lamari ya kawo rudani tare da haifar da kace nace akan yadda hakan ya kasance.

  Amma daga karshe kwamishinan gundumar na Kaoma Kennedy Mubanga ya shiga cikin lamarin inda ya umarci soji da yansanda suka kama akwatin gawar karfi da yaji kuma suka yi mata rakiya aka saka ta a cikin kabari aka binne ta.

  Dole yansanda suka yi ta harba barkonon tsohuwa kafin daga karshe aka sami sukunin shawo kan lamarin.Wasu matasa da suka harzuka da matakin na jami'an tsaro sun fasa gilashin motar wani dan jarida da yake daukan rahotu a wajen.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
 • Jam' iyar APC ta yi babban kamu, Ali Modu Sherif zai canja sheka zuwa APC

  By Isyaku Garba → April 26, 2018
  Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya ta bukaci Sanata Ali Modu Sheriff ya je mazabarsa a Ngala na jihar Borno domin ya yi rajistan kasancewa dan jam'iya.Sakataren watsa labarai na APC a Abuja Malam Bolaji Abdullahi ya ce jam'iyar ba ta karbar wadanda suka janja sheka a babban sakatariyar ta da ke Abuja.

  Sakamakon haka ya bukaci tsohon gwamnan na Borno ya je mazabarsa domin ya yi rijista.

  Abdullahi yana mayar da martani ne bisa wani labari a jaridu da ke nuna cewa tsohon gwamnan ya shirya tsaf domin ya canja sheka zuwa jam'iyar APC.

  Ali Modu Sheriff dai shi ne gwamnan Borno daga 2013 zuwa 2011.

  Ya kuma zama shugaban jam'iyar PDP na kasa na wucin gadi a 2016 a yanayi da ke cike da rudani da kalubale na shari'a wanda daga karshe bangaren Sanata Ahmed Makarfi da ke kalubalantar shi suka yi nassara a Kotu.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
 • An kashe Hausawa 11 tare da kone Masallatai 2 a sabon farmaki a Makurdi - Hotuna

  By Isyaku Garba →
  Akalla mutu 11 aka kashe yayin da aka raunata da dama bayan an kone wasu Masallatai biyu a wani hari da aka kai a kan al'umman Hausawa a garin Makurdi na jihar Benue.

  Mai ba gwamnan jihar Benue shawara kan harkokin addinin Musulunci Rilwanu Muhammed ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma yi harsashen cewa adadin zai iya zarce haka.

  Rilwanu ya ce akwai wasu karin mutum biyar wadanda ke kwance a Asibiti sakamakon raunuka da aka yi masu a lokacin  farmakin .

  Wannan ya faru ne bayan an kashe akalla mutum 16 ciki har da wasu Fada na Cocin Katolika guda biyu a jihar na Benue kwanaki biyu da suka gabata.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
 • Kalli Dino Melaye yana gaya wa yansanda zai kashe kanshi ya sa su cikin matsala !

  By Isyaku Garba →
  Wani hoton bidiyo ya bayyana wanda ya nuna Sanata Dino Melaye yana gaya wa yansanda cewa zai kashe kan shi ya sa yansanda cikin matsala.  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
 • Yadda wani mutum ke samun miliyoyin naira daga sana'ar kera bindigogi

  By Isyaku Garba →

  Ibrahim Manu wani mutum ne mai shekara 50 da ya fada hannun yansanda bayan an kama shi yana kera bindigogi.Manu ya ce yana samun miliyoyin naira sakamakon kera bindigogin da yake yi a kauyen Beji da ke karamar hukumar Bosso a jihar Niger.

  The Nation ta labarta cewa kera bindigogi gadon gidansu ne kuma shi bai san cewa haramtaccen sana'a bane.

  Kakakin hukumar yansanda na jihar Niger Muhammed Abubakar ya ce an kama Manu da shaidar ababe da yake amfani da su domin kera bindigogin kuma rundunar yansanda za ta gurfanar da shi a gaban Kotu.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
 • Kwacewar burki ya sa motar tipa ta markade yansanda 2 a jihar Delta

  By Isyaku Garba →
  Wasu jami'an yansanda guda biyu sun gamu da ajalinsu bayan wata motar tipa ta bi ta kansu sakamakon kwacewar burki.Nan take jami'an suka mutu bayan motar ta takesu a gadar Headon da ke garin Asaba na jihar Delta.

  Rahotanni sun ce yansandan na aikin sintiri ne a kan hanya, kwatsam sai burki ya gaza sakamakon haka motar ta kwace ta taho a guje ta bi ta kan yansandan su biyu.

  Fasinjoji da ke wucewa ne suka jaye gawakin yansandan daga kan hanyar mota.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
 • Dino Melaye sanye da ankwa a kan hanyarsa ta zuwa asibitin tarayya Abuja

  By Isyaku Garba →
  Hoton Sanata Dino Melaye kenan bayan yansanda sun garkama masa ankwa a hannu a kan hanyarsa ta zuwa Asibitin tarayya da ke Abuja.

  Dino Melaye dai yana fuskantar matsaloli sakamakon rashin yin ga maciji tsakaninsa da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

  Yansanda na nemansa bisa zargin daure ma ta'addanci gindi a jihar Kogi.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  Hoto: Sermna Shagari
 • Rikicin kabilanci ya yi sanadin mutuwar mutum 20 a jihar Nassarawa - Hotuna

  By Isyaku Garba → April 25, 2018
  Wani rahotu daga jihar Nassarawa ya nuna cewa an sami tashin hankali ranar Talata wanda yake da nassaba da kabilanci tsakanin  al'ummar Ebira da Bassa da basu ga maciji da juna a kauyen Ugya da ke karamar hukumar Toto a jihar Nassaarawa. Fiye da mutum 20 ne ake faragaban sun mutu sakamakon rikicin yayin da da dama suka sami raunuka.

  Rahoton ya kara da cewa kimanin yan babura 30 ne dauke da mutum 3 kowanensu suka kai hari a kauyen wanda daga bisani suka yi arangama da sojoji sakamakon haka sojoji suka rinjaye su.

  An kama da yawa daga cikin wadanda suka yi aika-aikan kuma suna hannun soji yayin da ake ci gaba da bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com