Yan sanda sun kama "Fatalwa" mai damfarar jama'a a jihar Arewa


Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu ta kama wani mutum mai shekaru 59 bisa laifin damfarar jama’a akai-akai.


 Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nguroje ya fitar, ta ce wanda ake zargin Muhammad Abubakar wanda aka fi sani da Malam Sabo, an ce ya saba da 419 wanda ya kware wajen damfarar jama’a ta hanyar da ba ta dace ba.


 ‘’Wanda ake zargin ya boye sunan sa yana mai nuna kamar fatalwa ne yana magana da wadanda yake yaudara da muryoyi daban-daban.  Wanda ake zargin, a wasu lokuta, yakan canza muryarsa ta zama kamar ta mace ko yaro don yin yaudara.  Kwanan nan ya yaudari wani Abba Bale na Demsawo kudi har dubu dari uku (N300,000)” inji kakakin ‘yan sandan.


 Nguroje ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da wuri.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN