Wata babbar kotu a Kano karkashin jagorancin Mai shari’a Halima Sulaiman ta yanke wa wata matar aure Rukayya Abubakar hukuncin daurin rai-da-rai, bisa laifin kashe dan kishiyarta. Daily trust ta rahoto.
Lauya mai shigar da kara, Barista Rabia Sa’ad, ta bayyana wa kotun cewa a shekarar 2021, Rukayya ta jefa yaron a cikin rijiya, lamarin da ya kai ga mutuwarsa.
A cewar Sa’ad, laifin da wanda ake tuhumar ta aikata ya sabawa sashe na 221 na kundin laifuffuka.
A yayin shari’ar, lauyan mai gabatar da kara ta gabatar da shaidu hudu a gaban kotun.
Lauyan wanda ake kara, Barista Rilwan Muhammad, ya roki kotun da ta yi wa wacce yake karewa sassauci domin uwa ce mai ‘ya’ya da dama da take kula da su.
Sai dai kotun ta umarci mai laifin da ta ci gaba da zama a gidan yari har tsawon rayuwarta a Duniya..
From ISYAKU.COM