Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ko su waye ba sun fille kan wani dan sanda mai suna Inspector Osang a jihar Akwa Ibom.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa wasu mahara sama da 10 ne suka kai wa mamacin hari a gidansa da ke kusa da Enen Afaha da kuma Afaha Ube, wani yanki da ke cikin birnin Uyo.
Wani ganau ya ce an yi ta harbe-harbe a yayin da mazauna yankin suka yi ta gudu domin tsira da rayukansu. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), Odiko Mac-Don, ya ce rundunar ta samu labarin kashe jami’an ‘yan sandan yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
"Mun sami wannan bayanin kuma lamari ne mara dadi. Tuni dai ana ci gaba da gudanar da bincike kuma mun himmatu wajen kawar da masu aikata laifuka a kan tituna. Har ila yau, ba mu karaya ba kuma mun himmatu wajen tabbatar da cewa, masu aikata laifuka za su fuskanci abin da suka aikata.” Inji majiyar.
From ISYAKU.COM