Yan bindiga sun kuma kai farmaki wata jihar Arewa, sun kashe mutane da dama


Wasu ‘yan bindiga a ranar Laraba sun kai hari a kauyukan Akinde, Tse Yongo, Tse Adem da Tse Ahikyegh a karamar hukumar Donga a jihar Taraba. Legit ya wallafa.

Harin ya kai ga kisan mutane uku yayin da mazauna yankin da dama suka samu raunuka daban-daban na harbin bindiga, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Wani shugaban Ugondo, Zaki Uma Ugondo, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa suna zargi wasu kamar sojoji ne tare da mayakan Jukun suka kai farmakin.

Zaki Ugondo ya ce da yawan 'yan bindigar na sanye da kakin sojoji, kuma suna haye kan babura na sojoji sa'ilin da suka farmaki kauyukan.

Ya ce:

“Sun zo ne a kan babura na sojoji sama da 30 yayin da yawancin su ke sanye da kakin soja, kuma suna dauke da muggan makamai.

"Da farko da mutanen kauye suka gansu, sai suka yi zaton sojoji suka zo, ba tare da sanin cewa 'yan bindiga ne da za su kashe su ba."

Ya shaida cewa, 'yan bindigar sun fara mamaye garin Akinde kafin su wuce zuwa Tse Yongo, sannan suka je Tse Adem da kuma Tse Ahikyegh.

Zaki Ugondo ya bayyana cewa sun kashe Luper Unongo, Tony Yongo da Gerigori Akinde, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN