Minista ya maida martani ga dattawan da suka yi barazanar Arewa zata juyawa Tinubu baya a 2027


Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle, ya maida martani ga ƙungiyar dattawan jihar Katsina kan tazarcen Bola Tinubu a 2027. Legit ya wallafa.

Matawalle ya yi fatali da kalaman ƙungiyar, inda ya ce ba ta da hurumin yanke shawara a madadin mutannen Arewa baki ɗaya, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Tun farko dai dattawan Katsina sun yi barazanar cewa Arewa za ta juya wa Tinubu baya a zaben 2027 saboda matakin da ya ɗauka na maida wasu sassan CBN zuwa jihar Legas.

Batutuwan da kungiyar dattawan Katsina ta nuna damuwa a kai sun haɗa da sauya wa wasu sassan babban banki wuri tare da hukumar FAAN da aikin faɗaɗa filin jirgin Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.

Dattawan dai kamar yadda rahotanni da dama suka nuna, sun bukaci shugaban kasar da ya janye matakin ko kuma ya rasa goyon bayan yankin Arewa a zaben 2027.

Yayin da yake shirin tafiya kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin tsaro na duniya a birnin Riyadh da yin Umrah, Matawalle ya ce barazanar da Dattawan Katsina suka yi ba komai ba ce.

Tsohon gwamnan Zamfaran ya ce wannan barazanar za ta iya haifar da ƙiyayya, rashin haɗin kai da sa ƴan Arewa su tsani ƴan uwansu na sauran sassan Najeriya.

Ya ce ba daidai ba ne dattawan su yi irin wannan gurɓatacciyar magana ta barna a madadin Arewacin Najeriya alhali sun san ba shi ne ra’ayin jama’ar yankin ba, rahoton Daily Post.

Matawalle ya bayyana cewa shugaba Tinubu na dukkan ‘yan Najeriya ne kuma ba shi da wata manufa ko ajanda ta yaƙar ko ɗaya daga cikin shiyyoyi shida na kasar nan.

“Saboda haka, ina shawartan dattawan Katsina su sauya tunani, su daina ɗaukar siyasa da zafi, su mayar da hankali kan abin da zai dunƙule ‘yan Nijeriya da ƙasa domin ci gaba," in ji shi.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN