Yan bindida da yawa sun baƙunci lahira yayin da sojoji suka dirar musu a jihar Arewa


Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda guda hudu a wani samame da suka saba kai wa a yankin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sashi na ɗaya ta hukumar sojin kasa a Najeriya, Laftanar Kanar Ibrahim Musa ya fitar. Legit Hausa ya wallafa.

Channels tv ta ce yayin wani sintiri cikin shirin ko ta kwana ranar Talata 6 ga watan Fabrairu, 2024 a Birnin Gwari, dakarun sojin suka yi gumurzu da ƴan bindigan.


Musa ya bayyana cewa yayin wannan artabu ne dakarun sojin suka yi nasarar tura ƴan bindiga 4 barzahu, sauran kuma suka ari na kare ɗauke da raunukan harbi.

Ya kuma ƙara da cewa sojojin sun kwato bindigogin AK-47 guda uku, mujallun AK-47 guda bakwai da kuma babura biyu daga hannun ‘yan ta’addan

Bayan haka, sojojin runduna ta daya da aka tura garin Birnin Gwari sun ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su ciki har da wani jariri ɗan wata tara a kauyen Kwaga a lokacin da suka yi arangama da ‘yan bindiga.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa an ceto mutanen ne tranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, bayan da sojojin suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar.

Rundunar ta bayyana sunayen mutanen da aka ceto da suka hada da Zakari Galadima, Ishaku Galadima, Habibu Illaysu, Nuzuli Ibrahim, Ramatu Aliyu da Ubaida Mubarak.

Sauran sune Zaliha Mubarak, Umma Haruna, Khairatu Salisu, Rahamatu Usman da kuma Rakiyia Yahaya, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

A cewarsa, an yi garkuwa da mutanen ne a ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu daga kauyensu da ke Masuku a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN