Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ayyana neman wani malamin addinin Islama a Bauchi, Dokta Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi, ruwa a jallo bisa zarginsa da cin zarafin kotu.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata takarda ta ‘yan sanda ta musamman da aka fitar a ranar Alhamis, 8 ga Fabrairu, 2024.
“Idan an gan shi, a kama shi a mikawa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ofishin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, sashin binciken manyan laifuka na jihar Bauchi, ko a kira lambar waya 08151849417, 09048226246,” ya kara da cewa, “Kyakkyawan tukuicin yana jiran kowane mutum da ya bayar da bayanin da ya kai ga kama shi," in ji shi.
Tun a shekarar 2022 ake shari'ar Sheikh Idris wanda ke fuskantar shari'a bisa zarginsa da kalaman batanci ga addini.
Sauran tuhume-tuhumen da malamin ke fuskanta kamar yadda babban mai shari’a kuma kwamishinan shari’a a jihar da ‘yan sanda suka shigar a babban kotun majistare sun hada da tada hankulan jama’a, cin zarafi ko kuma tada jijiyar wuya na addini.
Idris, a daya daga cikin wa’azin da ya yi, ya yi nuni da cewa zai tafi gudun hijira sakamakon barazanar da ya yi zargin Yana fuskanta daga gwamnan jihar, Bala Mohammed.
From ISYAKU.COM