Wasu matasa a garin Suleja na jihar Neja sun mamaye kan tituna a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu don nuna damuwarsu saboda tsadar kayan abinci a jihar.
Fusatattun matasan sun mamaye tituna suna kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta kawo karshen wahalhalu da hauhawar farashin kayayyaki da suke fama da su.
“Akwai wata zanga-zanga da ke gudana a karamar hukumar Suleja ta jihar Neja. Suna kira ga Tinubu da ya kawo karshen wahalhalun da talakawa ke fama da shi a kullum a kasar nan,” inji wani ganau
A ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu, maza da mata da matasa a Minna babban birnin jihar Neja su ma sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
From ISYAKU.COM