Gwamnan jihar Arewa ya koka bayan yan bindiga sun yi barazanar kai masa hari


Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ‘yan bindiga da ke addabar wasu sassan jihar na barazanar kai masa hari.


 Jaridar This Day ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Fabrairu, 2024, a yayin wani taron gaggawa na majalisar tsaro da aka fadada a gidan gwamnati, inda ya kara da cewa barazanar ‘yan fashin ya samo asali ne daga rahotannin tsaro.


 "Bisa rahotannin tsaro da muke samu, ina cikin wadanda 'yan bindigar ke tunanin kai wa hari, amma hakan bai yi min ba saboda Allah yana tare da mu, kuma zai kare mu," in ji Radda.


 Sai dai ya bayyana cewa barazanar da ‘yan ta’addan ke yi ba za ta hana gwamnatin sa daukar sabbin tsare-tsare na tsaro don magance ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro a jihar ba.


 Taron tsaron ya samu halartar shuwagabannin hukumomin tsaro na jihar da malaman gargajiya da na addini da manyan jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN