Matasa a jihar Osun a ranar Juma’a, 9 ga watan Fabrairu, sun gudanar da zanga-zangar lumana a Osogbo, babban birnin jihar, kan matsalar tattalin arziki da ake ciki a fadin kasar nan.
Zanga-zangar wacce aka yi wa lakabi da ‘Osun Peaceful Solidarity Walk’, ta gudana ne a gefen dajin Freedom da ke Osogbo. Masu zanga-zangar sun ce tsadar rayuwa ta zama abin da talaka ba zai iya jurewa ba.
Da yake zantawa da manema labarai, wanda ya shirya zanga-zangar, Kwamared Owolabi Hassan Oluwatobi, ya ce ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali sakamakon matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki.
Shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar, Kwamared Waheed Lawal ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya gaggauta magance matsalar tattalin arzikin kasar nan.