Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, 2024, ya ce ‘yan sandan sun kai farmaki maboyar ‘yan fashin inda aka yi artabu mai tsanani.
An bindige Isa Dei-Dei har lahira yayin da ‘yan kungiyarsa suka tsere da raunukan harbin bindiga.
“Da misalin karfe 1015 na HRS a ranar 5 ga watan Fabrairun 2024, jami’an DFI-IRT da ke aikin leken asiri, sun samu bayanai kan maboyar wasu ‘yan bindiga da suka yi kaurin suna a unguwar da ke cikin babban birnin tarayya Abuja, karkashin jagorancin wani Isa Dei-Dei kuma nan take jami'an suka je wurin wurin don su kama shi,” in ji sanarwar.
“Da suka hangi ‘yan sandan sai suka gudu, nan take jami’an suka bi su, lamarin da ya kai ga musanyar harbin bindiga mai zafi, ana cikin haka ne aka kashe fitaccen dan bindiga Isa Dei-Dei, yayin da sauran ’yan kungiyar suka yi nasarar tserewa. tare da raunukan harbin bindiga a jikinsu.
“Don haka muna kira ga jama’a musamman ma’aikatan lafiya da su ja hankalinmu ga duk wanda aka gani da raunin harbin bindiga domin ci gaba da bincike.”
From ISYAKU.COM