Babbar Kotu ta dakatar da shugaban APC na jihar arewa daga muƙaminsa, ta faɗi dalili


Babbar kotun jihar Benuwai ta haramta wa dakataccen shugaban All Progressives Congress (APC), Mista Austin Agada, nuna kansa a matsayin shugaban jam'iyya.

Kotun ta dakatar da Mista Agada daga ayyana kansa a matsayin shugaban APC ta jihar Benuwai biyo bayan dakatarwan da gundumarsa ta masa tare da wasu mambobi 6. Legit ya wallafa.

Wannan na zuwa ne yayin da alaƙa ta ƙara tsami tsakanin hadiman gwamnatin Benuwai da shugabannin jam'iyyar APC na jihar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

An tattaro cewa APC ta zargi shugaban ma'aikatan gwamnan Benuwai, Paul Biam da kwamishinan albarkatun ruwa, Climate Ugwu Odoh, da hannu a kai hari sakateriyar jam'iyyar.

A cewar jam'iyya mai mulki, kusoshin gwamnatin ne suka jagoranci ƴan sanda da sojoji suka kai farmaki sakateriyar a daidai lokacin da ake taron manema labarai.

Rikicin ya barke ne a lokacin da jami’an tsaro sanye da fararen kaya suka kutsa kai wurin taron manema labarai, inda suka far wa duk wanda suka gani.

Shugaban APC na gundumar Owukpa Ehaje ta 1 ya yi bayanin cewa sun je sakateriyar tare da dukkan shugabannin gundumarsa domin fayyace gaskiya.

Ya ce sun kira taron manema labarai ne da nufin nesanta kansu da waɗanda suka yi ikirarin dakatar da shugaban jam'iyya na jihar, Daily Post ta tattaro.

Amma Mista Agada ya shaida wa manema labarai cewa yunƙurin tsige shi da karfi da yaji daga matsayin shugaban jam’iyyar ne ya sa aka kai harin.

Ga dukkan alamu dai har yanzu akwai sauran rina a kaba a danbarwar da ke faruwa tsakanin APC da ɓangaren gwamnatin Benuwai karkashin Gwamna Alia.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN