Yadda saurayi mai shekara 22 ya siya motar N4.6m da alat na bogi


Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo ta kama Bakare Ayobami, dan shekara 22, da laifin siyan motar N.4.6m da alat banki na bogi. Kakakin rundunar ‘yan sandan, Funmilayo Odunlami-Omisanya, wacce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba a Akure, ta ce wanda ake zargin a ranar 20 ga Oktoba, 2023, ya je wurin siyar da motoci mallakar Mista Filani Oluwaseun da Mista Ogbaguwa Oluwasola.  a Ikare Road, Owo, domin siyan mota kirar Toyota Corolla 2006 akan kudi N4,650,000.00 ta hanyar amfani da alat banki na bogi. A cewar PPRO, ta hanyar tattara bayanan sirri, jami’an ‘yan sandan da ke aiki da rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ta musamman sun kama Ayobami Bakare da abokinsa, Abdullahi Abubakar mai shekaru 26 a Ekiti. “An gano motar da aka sace a garin Osogbo na jihar Osun, yayin da wata mota kirar Toyota Camry 2014 wacce kudinta ya kai Naira miliyan 6.2 da ake zargin an sace ta kuma aka samu daga hannun wanda ake zargin. “Sauran abubuwan da aka gano sun hada da iPhone 12 PRO Max guda daya wanda aka kiyasta kudinsa ya kai N600,000.00k da kuma iPhone 14 PRO guda daya, duk an siya su da alat na bogi,” inji ta. Odunlami-Omisanya, wanda ta bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya ce za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN