An kashe DCO da wasu mutane shida yayin da ‘yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda a Zamfara


Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in ‘yan sanda na rundunar ‘yan sanda da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, tare da kashe jami’in ‘yan sanda guda shida. Wani dan yankin mai suna Mohammed Ibrahim, ya shaidawa jaridar Punch cewa ‘yan bindigar da suke da yawa kuma dauke da manyan muggan makamai, sun mamaye garin Zurmi, hedikwatar karamar hukumar Zurmi da misalin karfe 5 na yammacin ranar Lahadi, 18 ga Fabrairu, 2024. An kuma tattaro cewa ‘yan bindigar sun kona shaguna da dama. Ibrahim ya ce nan take bayan ‘yan bindigar sun isa garin Zurmi ne suka nufi ofishin ‘yan sanda inda suka fara harbe-harbe kai tsaye, inda suka kashe DCO tare da raunata wasu jami’an ‘yan sanda a cikin lamarin kafin su banka wa ofishin ‘yan sanda wuta. A cewar ganau, ‘yan bindigar sun kai farmaki ofishin ‘yan sandan ne biyo bayan kashe mutanen su uku da ‘yan banga suka yi. “Kungiyar ‘yan banga sun je dajin tare da ‘yan sanda inda suka kai hari sansanin ‘yan bindigar kuma suka kashe uku daga cikin ‘yan bindigar tare da kama daya daga cikinsu,” inji shi. “Daga baya sun kashe dan fashin da suka kama bayan sun yi masa mugun duka. A dalilin haka ne ‘yan bindigar suka hada kansu da yawa suka nufi ofishin ‘yan sanda da ke Zurmi, a tunaninsu dan uwansu da ‘yan banga da ‘yan sanda suka kama yana hannun 'yan sanda. “Nan da nan suka isa ofishin ‘yan sanda suka bude wuta, inda suka kashe DCO tare da raunata wasu ‘yan sanda, sun shiga ofishin ‘yan sanda domin neman dan uwansu amma ba su gan shi ba, don haka suka banka wa ofishin wuta. "Kamar yadda nake magana da ku yanzu, jami'an soji sun isa garin yayin da 'yan fashin suka koma daji."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN