Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) ta cafke manyan motoci 15 dauke da kayan abinci a jihar Sokoto a kokarinta na hana fasa kwauri wanda ya ta’azzara tsadar kayayyaki a kasar.
Abubakar Chafe, mai magana da yawun hukumar NCS, Rundunar Sokoto, ya shaidawa manema labarai a ranar Asabar, 17 ga Fabrairu, 2024, cewa an tsayar da motocin ne a kan hanyar Gwadabawa-Illela.
Mista Chafe ya ce an yi kamen ne saboda yawan amfanin gonar da manyan motocin ke dauke da su.
Ya ce a halin yanzu manyan motocin na hannun hukumar kuma an fara bincike don gano masu kayan da inda za a aka kai kayan abincin.
Ya bayyana cewa rundunar hadin guiwa ta NCS Sokoto, da jami’an sashin ayyuka na tarayya da kuma sashin leken asiri na hukumar ne suka gudanar da aikin.
Mista Chafe ya kara da cewa aikin ya zama dole duba da hauhawar farashin kayayyakin abinci a kasar.
From ISYAKU.COM