An shiga har gidan wani magidanci aka masa kisar gilla da rana tsaka a Unguwar Badariya da ke garin Birnin kebbi jihar Kebbi.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa maharin mai suna Usman Muhammed ya je har cikin gidan Abubakar Abubakar inda ya kashe shi.
Mahaifiyar mamacin ta shaida wa manema labarai cewa maharin ya shiga gidan ne daga bisani ya farmaki mamacin da adda. Sai dai yunkurin da tsohuwar mai kimanin fiye da shekara 90 ta yi na rike addar ya sa maharin ya yi mata rauni a hannu da wasu sassa na jikinta.
Usman ya yi nassarar yanke Abubakar a wasu wurare a wuya kuma ya caka masa wuka a awaza da sauran sassa na jikinsa. Wannan mumunan lamari ya faru ne a gaban matar Abubakar da mahaifiyarsa mai yawan shekaru.
Yan sanda sun kama Usman Muhammed bayan farmakin da ya kai wa Abubakar Abubakar wanda ya zama ajalinsa.
Kakakin hukumar Yan sandan jihar Kebbi SP Nafi'u Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce Kwamishinan Yan sandan jihar ya umarci DPO na Yan sandan shiyar ya mika binciken zuwa sashin SCID na hedikwatar Rundunar na jiha don gudanar da binciken kwakwaf da kuma gurfanarwa a gaban Kotu.
Jami'an Yan sanda sun dauke gawar daga gidan don ci gaba da gudanar da bincike.
From ISYAKU.COM