Yakin Birnin Gwari: ‘Yan banga sun kashe ‘yan bindiga 40 a wani kazamin artabu da bindigogi


Wani kazamin tikici ya afku a dajin Katakaki da ke unguwar Kakangi a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan banga 19 na yankin tare da ‘yan fashi da dama. Legit ya wallaf
a.

 Wannan lamari, wanda ake kallon daya daga cikin mafi munin rikicin da ya barke tsakanin ‘yan banga da ‘yan bindiga a yankin Birnin Gwari, ya faru ne a makon jiya Asabar da misalin karfe 4 na yamma.

Rahotannin yankin na cewa, fadan ya barke ne kimanin kwanaki goma da suka gabata.


Majiyoyi sun bayyana cewa, an gwabza kazamin fadan ne lokacin da ‘yan bindigar suka far wa mutanen kauyen da ke aiki a gonakinsu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan bindiga sama da 40.

 Wani shugaban matasan yankin, Shehu Randagi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa an gano gawarwakin ‘yan fashi 19 a dajin.

 A lokaci guda sauran maharan sun gudu tare da abokan aikinsu da suka mutu, watakila don boye sunayensu.

 Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, ya ce:

 “Rikici ne da aka zubar da jini wanda ‘yan banga 19 suka mutu, yayin da wasu biyu suka bace.  Mun kuma gano gawarwaki 19 na barayin a cikin dajin Katakaki.

 “Mutanen kauyen Dajin Dogon Dawa da ke kusa da iyakar Jihar Neja, sun sanar da mu cewa sun kirga gawarwakin ‘yan fashin sama da 40 da abokan aikinsu ke jigilar su kan babura bayan arangamar.”

 Shehu Randagi ya kara da cewa mazauna yankin kudancin Birnin Gwari sun dogara ne da kare kansu daga ‘yan ta’adda saboda rashin sansanonin tsaro.

Shugaban kungiyar BEPU na masarautar Birnin Gwari, Ishaq Kasai, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa bayanan da suka samu sun nuna cewa ‘yan bindigar sun yi asarar rayuka sosai.

 A cewar Kasai, ‘yan bindigar sun far wa mutanen kauyen da ke aiki a gonaki, lamarin da ya kai ga yin arangama da ‘yan banga na yankin, wanda ya yi sanadin asarar rayuka a bangarorin biyu.

 Bugu da kari, ya yi tsokaci kan lalata manyan motoci da amfanin gona a yayin rikicin.

 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, bai bayar da amsa a hukumance ba, domin kokarin jin ta bakinsa ya ci tura har zuwa lokacin da muka samu rahoton.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN