Yan ta'adda sun kashe masu tafiya tsakanin yankin Kebbi da Zamfara


Rahotun VOA Hausa ta wallafa cewa duk da alamun samun saukin ayukkan 'yan bindiga da ake gani a wasu wurare na arewacin Najeriya, 'yan bindigar na ci gaba da neman sa'a, kuma wasu lokuta sukan samu, kamar yadda suka bude wuta ga wasu matafiya a wani kauyen da ke tsakanin jihohin Kebbi da Zamfara.

Bayanai sun nuna cewa bayan wadanda 'yan bindigar suka kashe hakama sun yi garkuwa da wasu da ba a san adadin su ba.

Murnar samun saukin matsalar tsaro na ci gaba da fuskantar cikas, domin har yanzu jama'ar wasu garuruwa da kauyuka suna cikin tsaka mai wuya saboda ayukkan 'yan bindigar.

Abinda ke nuna hakan shine wani hari da 'yan bindigar suka kai a kan wasu 'yan kasuwa da ke zirga-zirgar kasuwanci tsakanin kauyukan da suka hada jihohin Kebbi da Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya.

Shugaban Karamar Hukumar Wasagu/Danko ta jihar Kebbi, Hussaini Aliyu, da yake tabbatar da faruwar lamarin yace 'yan kasuwa ne daga jihar Zamfara wadanda ke amfani da wannan hanyar ta kauyen Dan Umaru 'yan bindigar suka tare kuma sun harbe mutane biyu.

Suma jama'ar garin Dan Umaru na Wasagu/Danko, kusa da inda aka kai harin, sun ce matsalar rashin tsaro ta jima tana hana su baci da idanu biyu rufe.

Shugaban Kungiyar Banga na mazabar Dan Umaru yace su kansu sun sha yin arangama da barayi saboda yadda suke haddabar jama'ar garuruwan dake yankin.

Kawo zuwa hada wannan rahoto, kakakin rundunar 'yan sanda bai dauki kiran da na yi masa ba, domin jin ta bakin rundunar.

Matsalar rashin tsaro dai a Najeriya a iya cewa tana kwan-gaba-kwan-baya domin ko an ga sauki sai matsalar ta dawo, su kuwa mahukunta kodayaushe kalamansu sune suna kokari sai dai matsalar ta ki tafiya baki-baya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN