Ni zan zama shugabanka da zarar ka shigo APC, Ganduje ya fadawa Kwankwaso


Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tunatar da kowa musamman jagoran Kwankwasiya, Rabiu Musa Kwankwaso cewa da zarar sun shigo APC, shi zai zama shugabansu. Legit Hausa ya wallafa.

Ganduje, a jawabin da ya yi cikin wani bidiyo da ya yadu, ya jadada cewa idan dai maganar jam'iyyar APC ake yi, shine lamba daya kuma mutum mafi muhimmanci.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto ya ce:

"Idan kana maganan APC ne mune shugabannin APC. Ba a kananan hukumomi ba, ba a jiha ba, ba shiyya ba amma a kasa baki daya.

"Idan kai dan jam'iyyar APC ne mai kati, kana karkashin shugaban jam'iyya na kasa. Haka shugabannin gunduma, jihohi da shiyoyi.

"Idan ka shigo APC yau, kana kasa da mu kuma kai mabiyinmu ne. Yana da muhimmanci ka lura da haka; dan gida da bako duk suna karkashin mai gida."

Ganduje, wanda ya yi wa taron yan jam'iyyar APC a Kano jawabi ya yi kira gare su kada su tada hankulansu ko su ji tsoron shigowar wani jam'iyyar APC.

Har ila yau cikin jawabinsa, Ganduje ya cigaba da cewa:

"Kamar yadda na fada muku, ko kai wanene kuma duk matsayinka ko da kai jagora ne, da ka shigo APC toh akwai kakanka a nan!".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN