Kotu ta umarci Donald Trump ya biya diyyar dala miliyan 83 ga wata marubuciyyaShafin BBC Hausa ya wallafa cewa wata kotun Amurka da ke New York ta umarci tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya biya diyyar dala miliyan 83 kan bata suna ga wata marubuciyya, E jean Carroll.

Hukuncin ya biyo bayan karar da Ms Caroll ta shigar cewa Mista Trump ya bata mata suna bayan karyata zargin da ta yi masa a kan cin zarafinta ta hanyar lalata kusan shekaru talatin da suka gabata.

A lokacin da alkali ke karanta hukuncin kotu matar da ke tuhumar tsohon shugaban na Amurka, E jean Carroll ta rike hannun lauyanta zaune a layin gaba a kotun.

Wannan hukunci ya farantawa matar rai wanda cikin shauki ta rungume manyan lauyoyinta biyu bayan alkali ya kamala karanta hukuncinsa.

Kotu ta samu Mista Trump da laifin bata mata suna bayan wasu kalamai a lokacin da yake kujerar shugabancin Amurka a shekarar 2019.

Ms Caroll ta bayyana yada wannan hali na Trump ke jefata cikin fuskantar barazanar kisa.

Kudin da kotu ta ce a biyata ya zarce dala miliyan 24 da ta nema sau hudu

A cikin sanarwar da ta fitar Ms Carroll ta bayyana hukunci a matsayin "babbar nasara ga mata kuma gagarumin shan kaye ga mai cin zarafi".

Sai dai tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ba ya cikin kotun a lokacin da alkali ya karanta hukuncinsa.

Tsohon shugaban ya fice daga kotun lokacin da lauyan Ms Carroll ke bayyanin karshe yana cewa tsohon shugaban kasar na nuna dabi'un fin karfin doka.

Bayan shari'ar, Mista Trump a shafinsa na X ya bayyana hukuncin a matsayin abin dariya da bita-da-kulin siyasa wanda ya zargi shugaba Biden da shiryawa.

Lauyarsa, Alina Habba ta ce za su É—aukaka kara saboda akwai lauje cikin nadi a hukuncin.

''Masu taya alkali yanke hukunci 'yan New york ne, shi yasa muke ganin akwai abubuwan da suka shafi bita-da-kulin siyasa karara kamar yadda ya kirasu kuma wannan na cikinsu.''

''Shi yasa aka gabatar da karar a jihohin da suka san cewa za su samu masa taya alkali yanke irin wannan hukunci.

"Sai dai wannan ba zai sa mu yi kasa a gwiwa ba kuma ina son na baku tabbacin cewa duk da cewa yau ba mu yi nasara ba, nan gaba za mu yi nasara saboda mun samu hujjar daukaka kara'', a cewar lauyar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN