Yadda mahara suka kona fadar babban Basarake kurmus, ya koka kan lamarin


A ci gaba da matsalolin tsaro da ke addabar al'ummar jihar Anambara, rahotanni na cewa wasu Yan bindiga sun sake gudanar da mugun aiki a gidan wani Basarake a jihar
.

Legit Hausa ya wallafa cewa wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne sun bankawa gidan mai sarautar gargajiya wuta a jihar Anambra.

Mai sarautar gargajiyar a kauyen Isseke da ke karamar hukumar Ihiala da ke jihar, Igwe Emmanuel Nnabuife ya tabbatar da lamarin.

Wannan na zuwa mako daya bayan ‘yan bindiga sun sace direban tsohon gwamnan jihar, Chinwoke Mbadinuju, cewar Premium Times.

Lamarin ya faru ne yayin da ya ke gudanar da bikin binne dan uwansa da ya rasu a kauyen Isseke.

Rahotanni sun tabbatar cewa direban ya gagara biyansu kudaden su kafin binne dan uwan nasa inda suka farmaki gidansa da dare.

Maharan sun durfafi gidan nasa inda suka ta harbi a sararin samaniya yayin da suka dauke shi zuwa wani da ba a sani ba.

Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Igwe Emmanuel Nnabuife ya ce maharan sun kona masa gidansa kurmus.

Ya koka kan yadda aka kai masa farmakin inda ya ce ba shi da matsala da kowa a yankin da za a yi masa haka, cewar Tori News.

Ya ce:

“Da gaske ne an kona mini gida kurmus wanda a yanzu haka na rasa komai da na sha wahalar nema a rayuwa, yanzu ba ni da gida.

“Komai ya kone amma nagode wa Allah babu rasa rai yayin lamarin da ya faru wanda ya tayar min da hankali.”
Kamishinan ‘yan sanda a jihar, Aderemi Adeoye ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka an fara bincike.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN