An cafke mai damfarar masu POS a wata jihar Arewa


Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani yaro dan shekara 17 mai suna Abdulmuminu Tasi’u bisa laifin damfarar wani mai sana'ar POS kudi N900,000 a karamar hukumar Maigatari da ke jihar.


 Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a karshen mako ya ce wanda ake zargin ya amince da aikata laifin kuma za a gurfanar da shi gaban kotu bayan bincike.


 “A ranar 03/01/24 da misalin karfe 1400, wani Aminu Mustafa ‘m’ mai shekara 38 a Unguwar Dodo quarters Maigatari karamar hukumar Maigatari mai sana’ar POS, ya kawo rahoto a ofishin ‘yan sanda na Maigatari cewa, a ranar da misalin karfe 1245.  Wani da ba a san ko wanene ba ya zo shagon sa na POS ya ciro kudi wanda bayan ya ba shi na’urar POS din ya yi amfani da shi ya zambace shi ya tura kudi naira dubu dari tara (N900,000.00k) a asusunsa.”


 “Da samun labarin, an sanar da ‘yan sandan da ke sintiri, an yi sa’a, an kama wani Abdulmuminu Tasi’u ‘m’ mai shekaru 17 da haihuwa a unguwar Adakawa da ke karamar hukumar Dala Jihar Kano, aka kawo shi ofishin domin gudanar da bincike.


 "Da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN