"Ta karewa Ganduje": Jigon PDP ya yi hasashen mataki na gaba da gwamnan Kano zai dauka bayan nasara


Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar, wani mamba a jam'iyyar PDP, ya yi hasashen cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ubangidansa a siyasa, Rabiu Kwankwaso, za su sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Abubakar, darakta janar na kungiyar Atiku, ya wallafa hakan ne a shafinsa na X a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, bayan Kotun Koli ta soke hukuncin da ya tsige Gwamna Yusuf daga kujerarsa

Jigon na PDP ya kuma ce hasashen komawar Gwamna Yusuf da Kwankwaso APC zai lalata siyadar shugaban jam'iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Ya rubuta:

"Ta karewa Ganduje! Ina da tabbaccin cewa Abba da Kwankwaso za su koma APC yanzu ko a nan gaba."

Ganduje ya yi aiki tukuru gabannin zaben 2023 don tabbatar da ganin dan takarar da yake so, Nasir Yusuf Gawuna, ya gaje shi.

Sai dai kuma, Gwamna Yusuf na jam'iyyar NNPP ya kayar da shi a zaben. Kokarinsa na ganin sun kwato kujerar gwamnan Kano ya tashi tutar babu yayin da Kotun Koli ta yanke hukunci a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

A halin da ake ciki, martanin jama'a kan hasashen Abubakar a dandalin X ya nuna cewa mutane da dama basu yarda da wannan batu nasa ba.

Diamond, @DareHardy09, ya ce:

"Wato kana tsammanin Tinubu zai sadaukar da Ganduje kan Kwankwaso?? A'a ba zai faru ba."

Captain Tango, @Capolutiti, y fada ma jigon na PDP:

"A kullun hasashenka cike yake da tangarda."

AMANOZEE, @AlasahMomoh, ya ce:

"Idan har Ganduje ne shugaban APC na kasa, Abba ba zai sauya sheka."

A baya Legit Hausa ta kawo cewa Kotun Kolin Najeriya ta da Abba Kabir Yusuf kan kujerarsa na gwamnan jihar Kano, a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Mai shari'a John Okoro wanda ya karanto hukuncin ya bayyana cewa kotun kasar ta yi kuskure a hukuncinta na rage kuri'u 165,616 daga adadin kuri'un da gwamnan ya samu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN