Yadda maciji mafi dafi na 2 a Duniya ya ciji budurwa tana tsakar barci a gadonta


Wata mata a Ostiraliya ta yi sa'a ta kasance a raye bayan da wani maciji mai tsananin dafi ya sare ta a lokacin da take kwana (barci) a gadonta.


 Matar mai shekaru 20 da ba a bayyana sunanta ba an saka ta a jirgin sama zuwa asibiti sakamakon harin da macijin da ake kira eastern brown, mafi dafi na biyu a duniya ya kai mata a gidanta mai nisa da ke yankin Western Downs a kudu maso gabashin Queensland.


 Macijin ya ciji matar ne a hannu da misalin karfe 1 na dare ranar Juma’a 12 ga watan Janairu.  Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan uwanta sun yi mata magani tun farko kafin jami’an lafiya su iso.


 Bayan da aka yi amfani da maganin kashe dafin, sai aka garzaya da matar zuwa Asibitin Toowoomba cikin kwanciyar hankali ta jirgin sama mai saukar ungulu na RACQ LifeFlight.


 Budurwar ta yi nasarar daukar hoton macijin wanda ya kutsa kai ya fito daga karkashin bargon ta.


 7News a Ostiraliya ta ba da rahoton cewa tana nan cikin kwanciyar hankali.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN