Tinubu ya dakatar da shirin NSIPS da gwamnatin Buhari ta kirkira


Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen da hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta kasa (NSIPA) ke gudanarwa, rahoton Leadership
.

Daraktan labarai a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ne ya sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu. Legit Hausa ya wallafa.

.A cewar Imohiosen, matakin ya kasance ne sakamkon binciken da ke gudana kan zargin badakalar kudade a hukumar da ma shirye-shiryen kansu, rahoton Daily Trust.

Ya ce an dakatar da gaba daya shirye-shiryen NSIPA guda hudu da suka hada da, shirin bayar da tallafin kudi ga marasa karfi, shirin GEEP, shirin N-Power da kuma na ciyar da yan makaranta na tsawon makonni shida.

Ya ce:

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma nuna matukar damuwa game da tangardar da aka samu na aiki da kuma badakalar da ke kewaye da biyan masu cin gajiyar shirye-shiryen.

“Saboda haka ya kafa kwamitin ministoci don gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumar da niyar ba da shawarar yin gyare-gyare da suka dace a hukumar NSIPA.

"A yayin dakatarwar nan, an daskarar da gaba daya ayyukan da suka shafi NSIPA, ciki har da taruka, biyan kudade da rijista."
Haka kuma, Shugaban kasar ya ba dukkan masu ruwa da tsaki da yan Najeriya baki tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da wani tsari cikin gaggawa da rashin son zuciya wanda zai tabbatar da cewa, a ci gaba.

Ya ce talakawan Najeriya za su amfana da wadannan tsari da za su gabatar wanda babu son zuciya a ciki.

A baya mun ji cewa hukumar NSIPA ta yi martani kan zargin badakalar kudi da ake yi wa ministar jin kai da kawar da talauci, Betta Edu.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, manajan labarai na NSIPA, Jamaludeen Kabir, ya yi watsi da ikirarin da ke alakanta ministar da badakalar kudi a hukumar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN