Sojoji zasu ƙara karbe ragamar mulkin Najeriya nan gaba? Tsohon shugaba soja ya feɗe gaskiya


Tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya ce yana da yakinin cewa ba za a sake samun katsalandan daga sojoji ba wanda zai kawo cikas ga dimokuradiyya a Najeriya. Legit Hausa ya wallafa.

Najeriya ta fuskanci kutsen sojoji da dama a siyasarta bayan samun ‘yancin kai, inda mazaje sanye da rigar kaki ke kifar da gwamnati su mulki kasar fiye da fararen hula gabanin 1999.

Babangida yana daya daga cikin sojojin da suka jagoranci kasar nan a wancan lokacin, inda ya yi mulki na tsawon shekaru takwas daga 1985 zuwa 1993

Da yake magana a wata hira da gidan talbijin na Channels cikin shirkn Inside Sources, tsohon shugaban ya ce mulkin soji ya sa Najeriya ta sami naƙasu daga asalin tsarin tarayya.

Ya kara da cewa zamanin da sojoji ke kutsa kai ciki harkokin siyasa ya zo karshe saboda ‘yan Najeriya sun kara gamsuwa ƙasar ta ci gaba da zama kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya

IBB ya ce:

“Ina ganin wannan shi ne (rashin cimma tsarin tarayya na gaskiya) daya daga cikin illolin da tabarbarewar gwamnatin soja ta haifar, ta dakile tsarin dimokuradiyya."

"Amma na yi imanin hakan ba zai sake faruwa ba, domin ‘yan Nijeriya sun kara sha’awar zama kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya a Afirka, dan haka ba na jim sojoji zasu ƙara karɓe mulki."

Sai dai ya ce a lokacin mulkinsa na soja, ya ‘yantar da tattalin arzikin kasar ta hanyar barin kamfanoni masu zaman kansu su zama cibiyar tattalin arzikin kasa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN