Mahaifiyar Abba ta hadu da maman Sanusi, an yi batun dawo da Sarki sarautar Kano


Mahaifiyar Mai girma Abba Kabir Yusuf ta kai ziyara wajen tsohuwar Mai martaba Muhammadu Sanusi II. Legit Hausa ya wallafa.

Wani bidiyo da Legit ta samu a dandalin sada zumunta ya nuna Khadijatul-Naja'atu Yusuf tare da mahafiyar Khalifa.

Hajiya Khadijatul-Naja'atu Yusuf ta ziyarci Hajiya Saudatu Hussain ne jim kadan bayan an ji hukuncin kotun koli.

Alkalan kotun koli sun tabbatar da Abba Kabir Yusuf ne zababben gwamnan Kano bayan watannin shari’a da APC.

Kamar yadda aka ji a bidiyon da hadimin gwamna, Abdullahi Ibrahim ya wallafa, tsofaffin sun yi wa Kano addu’o’i.

Wadannan Bayin Allah sun yi wa gwamna Abba Kabir Yusuf addu’ar samun nasara wajen jagorantar al’ummar Kano.

Maman gwamnan ta nuna akwai bukatar Sanusi II ya koma gidan sarauta domin cigaba da alherin da ya yi niyya.

Saudatu Hussain ce mahaifiyar Sarkin Kano na 14 watau Muhammadu Sanusi II wanda aka cire daga mulki a 2019.

Mai gidanta Aminu Sanusi ya rike sarautar Ciroman Kano kafin rasuwarsa, yana cikin ‘ya ‘yan Muhammadu Sanusi I.

Shi kuwa Sanusi I shi ne babban yaron Sarkin Kano Abdullahi Bayero da ya rasu a 1953.

Legit ta tuntubi Abdullahi Ibrahim, ya kuma tabbatar mata da cewa mahaifan jagororin na Kano sun hadu a jiya.

Abdullahi Ibrahim ya ce a ranar Juma’a ne maman mai gidansu watau gwamna ta ziyarci mahaifiyar Mai martaban.

Ana ta rade-radin gwamnatin Kwankwasiyya ta NNPP za tayi kokarin dawo da Muhammadu Sanusi II mulki.

Tun da za a rantsar da Abba, ya gayyaci Muhammadu Sanusi II zuwa wajen bikin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN