Sojoji sun ceto mutane 35 da aka yi garkuwa da su, sun kashe ‘yan ta’adda biyu a Katsina


Dakarun rundunar hadin gwiwa ta shiyyar Arewa maso Yamma Operation JIHADARIN DAJI (OPHD) da ke aiki a jihar Katsina sun ceto mutane 35 da aka yi garkuwa da su tare da kashe kashe ‘yan ta’adda 2 a wani aikin bincike ceto da suka gudanar.


 Kyaftin Yahaya Ibrahim, jami’in yada labarai na Operation HADARIN DAJI, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 30 ga watan Janairu, 2024, ya ce an samu nasarar hakan ne a ranar 27 ga watan Junairu, 2024, a lokacin da aka kai samame ga wasu sansanonin ‘yan ta’adda da aka gano a dajin Dumburum.


 Sanarwar ta kara da cewa "A yayin farmakin sojojin sun yi arangama da 'yan ta'addar dauke da makamai, inda suka kashe 2 daga cikin 'yan ta'addan yayin da wasu suka tsere da mummunan raunukan harbin bindiga."


 “Wadanda aka ceto sun hada da maza 19, mata 12 da kuma yara 4, nan take kwamandan runduna ta 17 Brigade Nigerian Army/Sector 2 Operation HADARIN DAJI, Birgediya Janar OA Fadairo, ya mika wa gwamnatin jihar Katsina mutanen.  Tare da alkawarin kai farmaki kan yankunan 'yan ta'adda."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN