Kuncin rayuwa a Najeriya ya sa tsohon soja ya rataye kansa har lahira


Wani tshon soja mai shekaru 72 mai ritaya mai suna Francis Dooga, ya kashe kansa a Makurdi, babban birnin jihar Benue. Ana zargin marigayin ya rataye kansa ne a kan wata bishiya a gidansa da ke daura da cocin St. Joseph Catholic Church a Iniongun, a unguwar Makurdi da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, 2024. Wani makwabcin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Dooga wanda aka fi sani da ‘tsohon soja’ ya dauki wannan mummunan mataki ne a yayin da ‘yan uwa ba sa gida. Wasu mazauna yankin sun yi zargin cewa tun da farko marigayi mai ritaya ya koka da halin kunci. An kuma tattaro cewa marigayin ya koka da cewa daya daga cikin ‘ya’yansa yana zare kudin fanshonsa da zarar an biya shi. Ya kuma koka akan rashin samun kudaden fansho da yawa daga hukumar fansho. “Kafin ya kashe kansa, mutumin ya kasance yana korafin kudin sa na tsaro (SDA) da gwamnatin tarayya ta ba hedikwatar tsaro, wanda kuma aka sake shi ga hukumar fansho ta sojoji.” Inji wani mazaunin garin. “Ya ce ana biyansu kudaden fansho ne kadan a maimakon a rika biyansa kudin da yawa a kowane wata, wanda hakan ya haifar masa da tsananin talauci kuma ‘yan uwansa suka yi watsi da shi.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN