Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta wallafa sanarwar cigiyar wannan yaro mai suna Abdurrahaman dan Unguwar Kofar Kola a garin Birnin kebbi. Suna cigiyar wannan yaro wanda yake da matsalar Jinnu kuma ya bar gida watanni uku da suka gabata ba labarinsa.
Hisbah ta wallafa cewa:
A wannan karon ya kwashe tsawon wata 3 ba shi ba labarin sa, wani lokaci Bai magana ko ya fadi gari ko unguwar da ba tasu ba Don haka Ake rokon jama'a dasu taimaka da duk Wanda Allah yassa yagamshi ko yaji labarinsa a sanar da hukumar Hisbah ta jihar kebbi ko fadar Amiru zoramawa Alh bello Ibrahim Nahaliku ko wata hukuma Mafi kusa ko a tuntubi mahaifiyarsa a unguwar kofar kola dake Nan Birnin Kebbi jama'a ataimaka Muna da sharing ko Allah zaisa adace
Allah ya sa adace ameen"
From ISYAKU.COM