Kungiyar tsaro ta Western Nigeria Security Network (WNSN) da aka fi sani da Amotekun ta kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da tono wata gawar da aka binne a garin Saki cikin karamar hukumar Sakiwest ta jihar Oyo.
An kama wadanda ake zargin ne a ranar Talata, 9 ga watan Janairu, 2024.
Daya daga cikin wadanda ake zargin ya je makabartar ne a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, domin tono, Kuma ya sare kan gawar da aka binne a ranar.
An kama su kuma wani faifan bidiyo ya nuna su na ikirari da aikata laifin.
Wata majiya ta ce, wadanda suka aikata laifin suna zaune ne a unguwar Oba Abimbola layout, kusa da Ogboro Road a garin Saki. Amotekun ne suka kama matashin mai matsakaicin shekaru da kawuna guda biyu da ya sare na gawaki da ya tone a kabarinsu.
Kalli bidiyon a kasa.
From ISYAKU.COM