NAF ta halaka Janari hatsabibin jagoran masu garkuwa da mutane a KadunaAn kashe wani mai garkuwa da mutane da aka fi sani da Janari tare da tawagarsa a hare-haren da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama.


 Kakakin hukumar ta NAF, Air Vice Marshall, Edward Gabkwet, ya ce an kashe Janari da makarraban sa ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, a wani wuri kusa da Gadar Katako a karamar hukumar Igabi.


 Ana zarginsu da kai hare-hare da sace-sace da dama a cikin jihar Kaduna da kuma kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.  An ba da izinin kai hare-hare ta sama bayan da aka ga Janari da ‘yan kungiyarsa a wani wuri kusa da Gadar Katako a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.


 Sanarwar ta ce;


 “Bayan bayanan da aka samu sun nuna cewa lallai an kawar da Janari tare da wasu ‘yan ta’adda/ masu garkuwa da mutane da dama.

 “An kuma kai irin wannan harin ta sama a ranar 20 ga watan Janairun 2024 akan maboyar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a kusa da Chukuba a jihar Neja tare da samun nasarori daban-daban.

 "Bayanai da aka samu bayan hare-haren ya nuna cewa bayan halaka Yan ta'addan, an kuma lalata karfinsu na motsi da ababen hawansu.."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN