Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wasu mutane uku da ake zargi Augustine Ikponmwoba (62) da Roland Ibizugbe mai shekaru 63 da kuma Blessing Joseph mai shekaru 36 bisa zargin satar motoci biyu a yayin wani taron ibada coci.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin tare da wasu da ake zargi da aikata laifuka, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP, Funsho Adeboye, ya ce an kama su ne bayan bin diddigin wayar da aka sace tare da motocin da daya daga cikin wadanda ake zargin ya baiwa budurwarsa, Blessing Joseph, a matsayin kyauta.
CP ya ce Misis Joy Mordi da Mista Peter E. Abiwo sun kai wa ‘yan sanda rahoton cewa sun ajiye motocinsu a filin tunawa na Garrick don halartar wani ibadar coci, kuma bayan da suka gama ibada sun gano cewa an sace motocinsu, A lokacin bincike, an kama matar da ake zargin, Blessing Joseph, wacce ke rike da wayar da aka bari a motar Mordi.
Adeboye ya ci gaba da cewa Blessing ta amsa cewa abokinta mai suna Augustine Ikponmwoba ne ya ba ta wayar.
"Kamen Ikponmwoba ya kai 'yan sanda zuwa Roland Ibizugbe wanda shi ma aka kama. Wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikata kuma za a gurfanar da su a gaban kotu."
From ISYAKU.COM