A karon farko a tarihi, mace ta zama shugabar ƙaramar hukuma bayan lashe zabe a jihar arewa



A karon farko a tarihi, an samu macen da ta zama zababbiyar shugabar ƙaramar hukuma guda a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas. Legit Hausa ya wallafa.

Hukumar zaɓe ta ayyana Hajiya Inna Galadima ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wadda ta lashe zaɓen karamar hukumar Jere a Borno, rahoton Daily Trust.


Baturen zaɓen ƙaramar hukumar, Farfesa Mohammed Konto, shi ne ya ayyana Galadima, tsohuwar kwamishina da mai bada shawara a matsayin wacce ta ci zaɓen.

Konto ya ce ƴar takarar APC ta samu kuri’u 110,459 inda ta kayar da babban abokin hamayyarta na Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri’u 2,478.

Ranar Asabar da ta gabata, 20 ga watan Janairu, 2024 aka gudanar da zaɓen kananan hukumomi 27 da kansiloli sama da 300 a jihar Borno wadda APC ke mulki.


Rahoton The Cable ya nuna cewa jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe zaɓukan kujerun ciyamomi a sauran kananan hukumomin jihar Borno guda 26, duk da wannan 27 kenan.

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (BOSIEC), Alhaji Lawan Maina, shi ne ya sanar da haka a sakamakon da ya bayyana ranar Lahadi a Maiduguri, baban birnin jihar.

A jawabinsa bayan kammala tattara sakamako, Alhaji Maina ya ce:

"All Progressive Congress (APC) ta samu nasarar lashe kujerun ciyamomi 27 da ke faɗin jihar, haka nan kuma ita ta samu nasara a zaɓen kansiloli 312."


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN