Abun mamaki: Yadda Karuwa ta kwace bindigar mai gadi bayan ya kasa biyanta kudin yin lalata da ita


Karuwa ta kwace bindigar wani mai gadi mai shekaru 27, mai suna Evidence Mangonono sakamakon kasa biyanta kudinta bayan sun yi lalata. 


 Lamarin ya afku ne a kusa da wani banki inda aka baiwa Mangonono aikin gadi.  An gabatar da lamarin a gaban Kotun Majistare ta Mutoko, inda Alkalin Kotun, Chiedza Gatsi ya jagoranci shari’ar a kasar Zimbabwe.


 A cewar mai gabatar da kara karkashin jagorancin Nathan Majuru, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu lokacin da Mangonono, tare da abokan aikinsa, suka sha maganin karfin maza don ya kara masu kuzari wajen jima'i.


 Bayan haka, Mangonono ya je ya nemo Karuwa  wanda aka bayyana sunanta a matsayin Choice, kuma ya kai ta a gefen bankin inda yake aiki a matsayin mai gadi ya shakata da ita.


 Sai dai bayan Mangonono ya gaza cika kuɗi da suka yi alkawari da Choice,  sai ta ɗauki bindigarsa a matsayin garantin cinikin da ba a biya ba watau (jingina).


 Asiri ya fara tonuwa ne bayan shugaban wajen da Mangonono ke aiki ya gano babu makamin hidimarsa na aiki kuma cikin gaggawa ya kai rahoton lamarin ga 'yan sanda.


 Alkalin kotun Gatsby ya yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ga Mangonono tare da dakatar da shi bisa sharadi.  A karkashin sharuddan dakatarwa, Mangonono zai yi hidimar al'umma na sa'o'i 325 a makarantar firamare ta Hurungwe da ke garin Murewa a kasar ta Zimbabwe.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN