Yan bindiga sun sace dan kasuwa sun harbe wani mutum a Sokoto


An yi garkuwa da dilan kayayyakin gyaran motoci tare da harbin wani mutum daya a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari tashar Motar Tambuwal da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar Sakkwato.


 Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar, 27 ga watan Janairu.


 Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun bayyana isowarsu ta hanyar harbe-harbe.


 Sun kai hari a wani shagon sayar da kayayyakin gyaran motoci inda suka yi awon gaba da mai shi, Mista Paul Ndibusi Okula.  Hakazalika sun jikkata wani mutum daya wanda a halin yanzu yake jinya a asibiti.


 Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun fito ne domin yin garkuwa da mahaifin dan kasuwar amma tun da ba ya nan a lokacin da suka kai harin, sai suka tafi da dansa.


 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya kara da cewa ‘yan sandan na nan suna bin ‘yan bindigar.


 “Kun san Tambuwal gari ne mai wucewa tsakanin Jihar Sakkwato da Jihar Kebbi.  Mun sanar da ‘yan sanda da ke makwabtaka da jihar Kebbi yayin da ake ci gaba da bincike,” inji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN