Kotun Koli: APC sun hango nasara, 'shirin' rantsar da Gawuna ya kankama a Kano


Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta na kyautata zaton yin nasara kan NNPP a kotun koli a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano. Legit Hausa ya wallafa.

Premium Times ta ce magoya bayan APC na reshen Kano sun fara rabon ankon kayan da za a sa ranar rantsar da Nasiru Yusuf Gawuna.

Hakan yana zuwa ne bayan ‘ya ‘yan APC sun yi azumi da salloli da addu’o’i domin su sake samun galaba a kan Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Rahoton ya ce tun a karshen makon jiya mabiya APC su ka fara rabon kayan anko a yankin Fagge a birnin Kano domin shirin rantsuwa.

‘Yan APC sun ci burin cewa Nasir Gawuna zai zama gwamna bayan tsige Abba Gida Gida a kotun koli, inda gwamnan ya daukaka kara.

Ana tunanin cikin makon nan alkalan kotun koli za su raba gardamar shari’ar zaben Kano.

Wani Faisal Ibrahim ya ce ya yi dinkin kayansa kamar sauran ‘yan APC, su na jiran lokacin da za a rantsar da Gawuna ya zama sabon gwamna.

Faisal Ibrahim yana ganin alkalan kotun koli za su ba lauyoyin jam’iyyar APC gaskiya.

Jagororin APC a Fagge irinsu Ahmad Dangwarzo sun raba wannan anko, sun ce idan dai ba a canza tsarin mulki ba, APC ta karbe mulkin Kano.

Legit ta fahimci akwai wadanda su ka tanadi rigunan GawunaHasArrived G & G da za a ci kwalliya da su idan za a rantsar da sabon gwamna.

A bayan wadannan riguna an rubuta Sashe na 177, ma’ana sashen dokar da kotun daukaka kara tayi amfani da shi wajen tsige Abba a 2023.

Ana da labari kotun korafin zabe da na daukaka kara sun ba Nasir Gawuna nasara a zaben Kano da aka yi a 2023, aka rusa nasarar NNPP mai-ci.

A dalilin hakan ne zanga-zangar lumana su ka barke a wasu wurare a jihar Kano.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN