Talaka zai shiga tasku a Najeriya, MTN, Glo, Airtel za su kara kudin data


Kamfanonin sadarwa na neman gwamnatin tarayya ta ba da damar karin kudin katin waya da data na hawa intanet a kasar nan.

Majiyoyi daga NCC da Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani sun shaida wa Daily Trust cewa, masu amfani da layukan waya a Najeriya za su biya Karin 10% zuwa 15% fiye da kudin da suke siyan data a yanzu idan bukatar kamfanonin ta tabbata. Legit Hausa ya wallafa.

Tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, kamfanonin sadarwa suka roki gwamnati da ta amince da bukatarsu ta sake yin bitar farashin kudaden kira da data.

Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanonin sadarwa ba su kara farashinsu ba tsawon shekaru duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake samu a kasar.

A halin yanzu, wasu sun lura cewa kila kamfanonin sun kasance suna rage karfi da juriyar data don rufe wannan gibi na rashin Karin farashi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar masu lasisin sadarwa ta Najeriya (ALTON) ta bayyana a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023, cewa tsarin kudin kira da data a yanzu ba zai kaisu ga madakata ba.

Sai dai har yanzu gwamnati ba ta biya bukatarsu ba har sai an fara aiki da kasafin kudin shekarar 2024 gadan-gadan, kamar yadda wata majiya ta shaida wa The Cable ta ruwaito.

A cewar majiyar, ana ci gaba da nazari da tattaunawa kan yadda karin ba zai shafi talakawan Najeriya ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN