Dakatacciyar Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu ta sha kunya bayan hana ta shiga wurin Tinubu. Legit Hausa ya wallafa.
Edu ta zo fadar shugaban kasar ce a Abuja jim kadan bayan an dakatar da ita inda ta ke neman ganawa da shugaban, cewar Tribune.
Yayin da ta wuce dukkan shingayen jami'an tsaro, an dakatar ta ita daga ganin Shugaba Tinubu a cikin ofishinsa.
Har ila yau, bayan an hana ta ganin shugaban, jami'an tsaron sun kuma kwace katin shaidar shiga fadar daga gare ta.
Daga bisani kuma jami'an tsaro sun fitar da ita daga fadar a cikin wata mota kirar Toyota Hilux ta fadar Aso Rock.
From ISYAKU.COM