Bayan da Kotun koli ta yanke hukuncin tabbata da Abba Kabir na jam'yyar NNPP a matsayin zababben Gwamnan jihar Kano ake ci gaba da yin sharhi kan lamarin.
Shafin Labarai na Legit ta wallafa cewa wani jigo a Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Honorabul Ibrahim Danlami Kubau, ya yi magana kan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.
Honorabul Danlami ya yi takarar kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ikara da Kubau, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP a babban zaɓen 2023.
A yayin wata tattaunawa da Legit Hausa, Danlami ya nuna farin cikinsa kan hukuncin da Kotun Kolin ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf, matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano.
Ya bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga dimokuraÉ—iyyar Najeriya, domin ya ceto ta daga faÉ—a wa cikin ruÉ—ani.
Ya nuna cewa da Kotun Kolin da amince da hukuncin da kotun zaɓe da Kotun Daukaka Kara, suka yi na soke ƙuri'un da APC ta yi zargin ba ingantattu ba ne, da ta buɗe ƙofar da wasu za su iya yin hakan a nan gaba.
Da aka tambaye shi ko meyasa Shugaba Tinubu bai tsoma baki domin APC ba a shari'ar zaɓen ba, sai ya kada baki yace:
"Ba maganar APC ba ne, magana ce ta Najeriya, Æ´an Najeriya da dimokuraÉ—iyya, mutane sun riga da sun san abin da suke so, ba zai iya sanya baki domin APC ba saboda al'ummar Kano sun riga da sun yi watsi da APC"
"Ba zai iya sanya baki domin APC a Kano ba domin tuntuni mutanen Kano sun sauka daga layin APC, mutane suna son sabuwar fuska, mai sabon tsari da sabon fata, wanda hakan ne ya sanya suka zaɓi wasu ƴan takara a Kano, Bauchi, Zamfara da wasu sauran jihohin."
From ISYAKU.COM