Pantami ya samo wanda zai biya kudin fansa a sako 'yan uwan Nabeeha da aka sace a Abuja

Legit Hausa ya wallafa cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana yadda ya kawo hanyar sharewa ahalin Nabeeha hawaye bayan samo wanda zai biya kudin fansan da ‘yan bindiga suka nema bayan sace su.

Idan baku manta ba, an ruwaito yadda wasu ‘yan ta’adda suka yi awon gaba da wasu ‘yan gida daya ‘yan mata shida, inda suka nemi kudin fansan miliyoyin kudade.

Wannan lamari ya dauki hankalin ‘yan Najeriya da dama, musamman ganin ya faru ne a babban birnin tarayya Abuja, inda ya fi ko ina tsaro a kasar.

Da yake bayyana yunkurin taimakawa ahalin da suka shiga jimami, babban malamin addinin Islama, tsohon minista kuma mai fada a ji a Najeriya, Farfesa Pantami ya samar da mafita.

Ya bayyana cewa, ya magantu da abokinsa da ya amince da biyan akalla Naira miliyan 50 don tabbatar da an sako wadannan ahali da ke hannun ‘yan ta’adda.

A bayaninsa, ya ce sam ba ya goyon bayan a ba ‘yan ta’adda kudaden fansa, amma yanayi ya nuna an cutar da ahalin kuma ya kamata a yi hubbasa don taimaka musu.

A jawabinsa da ya yada a kafar Twitter, Pantami ya ce:

“Ni kaina ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda. Sai dai kuma tunda ta tabbata jiya mun rasa ‘yarmu Nabeeha, kuma an yiwa sauran yaran 5 barazana kamar yadda na yi magana da mahaifinsu jiya da yau.

“Don haka, na yi magana da wani abokina kuma ɗan’uwa wanda ya amince zai biya sauran Naira miliyan 50 na miliyan 60 din nan take.

“Na ba da lambar asusun mahaifin ƴan matan mai suna, Mansoor Al-Kadriyar, ga abokina kuma dan uwa don aikawa da kudin kai tsaye. “

Pantami ya ba da shawari da ishara ga mahaifin ‘yan matan da cewa:

“Duk wani karin kudin da aka samu ya zuwa jiya, sai uban ya yi amfani da shi wajen yiwa yaran da sauran 'yan uwa a ahalin jinya da yardar Allah.

“Allah Ta'ala Ya sakawa wannan aboki kuma dan uwa da Jannatul Firdaus bisa wannan gudummawar. Ya kuma sakawa duk wadanda suka bada gudumawa ta kowace hanya da Jannatul Firdaus.

“Ya kuma gafartawa Nabeeha, ya kubutar da ‘yan uwanta. Allah kuma ya taimaki jami'an tsaronmu wajen kawo karshen wannan kalubale. Allah ya sa Najeriya ta zama wuri mafi alheri garemu baki daya.”Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN