Hisbah jihar Kebbi ta gano dan babur da aka raunata aka jefar a Zauro


Daga karshe an gano sunan mutumin da hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta bayar da cigiya bayan wasu da ba a san ko su waye ba suka raunata shi suka jefar da shi.

Hisbah ta gano cewa sunan shi Usman dan kauyen Magun a gundumar Dalijan da ke karamar hukumar Gwandu a jihar Kebbi.

Kazalika Hisbah ta ce Usman yana sana'ar Kabu-kabu ne kuma ana kyautata zaton cewa barayin mashin ne suka 'halaka' shi suka jefar da shi a Zauro kan hanyarsa ta komawa garinsu.

Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta wallafa cewa:

"AN GANE DANGIN WANDA MUKA BADA CIGIYARSA 

Ansamu labarin mutumen da muka Bada cigiyarsa sunan sa Usman Dan kyauyen magun ne gundumar dalijan gwandu local govt kebbi state

Usman sanaar kabu kabu yakeyi ana saran barayin nashin ne suka hallaka shi suka yi jifa dashi a zauro hanyarsa ta komawa kyauyensu yanzu haka Yan uwansa sun zanta damu akan zowa daukar sa don cigaba da ayimasa jinya
Allah sauwaka ya kiyaye ya kare Ameen Allah bashi lafiya ameen"

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN