Daga zuwa yin jarabawar shiga makarantar firamare, Hedimasta ya yi wa yar shekara 6 fy*de


Mai shari'a Nana Fatimah Jibrin, shugabar babbar kotun jihar Bauchi mai lamba 11, ta yanke hukuncin daurin shekaru 11 a gidan kaso ga wani Hedimasta a garin Burra da ke karamar hukumar Ningi mai suna Jalaludeen Zakari bisa samunsa da laifin yin lalata da wata yarinya yar shekara 6.


 Yarinyar ta kasance a makarantar don yin jarabawar shiga makarantar amma Zakari ya tsare ta tsawon sa’o’i bayan an rufe makarantar a hukumance.


 Barista Dayabu Ayuba, lauya mai shigar da kara kuma lauyan jiha a ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata, 2 ga watan Janairu, 2023, ya ce wanda ake tuhumar ya shigar da yatsarsa a cikin al’aurar yarinyar.


 Ayuba ya ce a lokacin da ake shari’ar, shaidu uku ciki har da wanda aka yi wa lalata, sun ba da shaida a gaban kotun.


 “Mai laifin ya bukaci yarinyar da ta tsaya, ya sallami sauran daliban bayan an tashi daga makaranta, ba tare da bayar da dalilin tsawaita zaman yarinyar ba.  Yayin da aka bar ta a baya, Hedimasta ya ya kai mata harin lalata, wanda ya yi daidai da fyade a shari’ance,” inji shi.


 Ayuba ya ce an yanke hukuncin ne a watan Yulin wannan shekara bayan Jalaludeen ya roki kotu da ta yi masa sassauci.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN