An saki shugaban karamar hukuma da aka sace tare da jama'arsa bayan an biya kudin fansa, duba ka gani


Shugaban karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa, Safiyanu Isa Andaha, da uban gidansa na siyasa, Adamu Umar, da wasu mutane biyu da aka sace sun samu ‘yanci bayan an biya kudin fansa N10m.


 LIB ta ruwaito cewa ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wadanda aka sace a ranar sabuwar shekara a kauyen Ningo da ke kan titin Andaha-Akwanga.


 Wani na kusa da shugaban karamar hukumar, wanda ya tabbatar wa da Daily trust faruwar lamarin, ya ce an sako wadanda abin ya shafa ne a bayan wani tsohon gidan mai da ke hanyar Bayan Dutse da ke wajen garin Andaba a daren ranar Talata, 2 ga watan Janairu, 2023.


 “An sako su ne a daren ranar Talata da misalin karfe 9 na dare a kan hanyar Bayan Dutse kuma an biya su kudi N10m a matsayin kudin fansa,” inji majiyar.


 Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa, wani mamba a kwamitin aiki na jam’iyyar All Progressives Congress na jihar wanda ya fito daga karamar hukumar Akwanga kuma ya jagoranci tattaunawar ya tabbatar da sakin bayan da ya nemi a sakaya sunansa.


 Shugaban karamar hukumar da sauran wadanda abin ya rutsa da su sun samu rakiyar jami’an tsaro ne zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) dake garin Keffi domin kula da lafiyarsu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN