Gwamnan Sokoto ya ja kunnen wani kampani kan hanyar Gandi, ya yi barazanar kwace kwangilar (Bidiyo)


Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto na jihar Sokoto ya nuna rashin jin dadi da yadda kamfanin da ke kwangikar hanyar Gandi ke gudanar da aikin hanyar.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar bazata da ya kai a wajen da ake gudanar da aikin.

Gwamnan ya ce a shafinsa na X:

"Na umarci kamfanin kwangila na ZBCC da ke kula da aikin hanyar Gandi da gwamnatina ta bayar da su koma wurin ko kuma a soke aikin daga hannunsu".  

"Aikin  hanyar dai an bayar da shi ne watanni biyu da suka gabata amma har yanzu ba a samu ci gaba sosai a wurin ba".  

"Tun  lokacin da muka ba dan kwangilar da kudaden fara aiki, amma abin da na gani a yau bai burge ni ba, saboda ina tsammanin in gan fiye da abin da aka yi".  

"Na  sha fada a baya kuma bari in sake cewa gwamnatina ba za ta karbi duk wani aikin da bai dace ba ko mara inganci daga kowane dan kwangila ba".  

"Don  haka ina umurtar dan kwangilar da ya dawo wurin da sauri ya kammala aikin a cikin lokacin da aka kayyade ko kuma ya fuskanci mummunan sakamako".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN