Tsakanin Abba da Gawuna: An hango wanda zai yi nasara a kotun koli duba da wasu dalilaia


Kungiyar tsofaffin mashawarta a a APC ta ce akwai 99.9% cikin 100% na kyautata zaton samun nasara a hukuncin kotun koli da ake jira a kan rikicin zaben gwamnan Kano. Legit Hausa ya wallafa.

Shugaban kungiyar Dakta Abbati Bako ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da yake taya dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule Garo murnar nasara, ya ce ko shakka babu hukuncin da aka yanke a baya zai samu a kotun koli.

A cewarsa:

“Ina son amfani da wannan dama wajen taya zababben gwamnanmu Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule Garo murna a zaben da ya gabata kamar yadda kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara suka bayyana.”

Ya kuma bayyana cewa, da yawan mutanen jihar Kano na Allah-Allah Gawuna ya samu nasara a kotun kotun

A cewarsa, suna tsammanin samun mulki na gari daga dan takarar na jam’iyyar APC mai mulkin kasa a yanzu.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana game da shari’ar Kano, inda wasu ke ganin ba a yiwa jam’iyyar NNPP adalci ba kwata-kwata, New Telegraph ta tattaro.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN