Wanna na kunshe ne a cikin sanarwa da suka wallafa a shafukansu na X a yau Litinin 1 ga watan Janairu. Legit Hausa ya wallafa.
A martaninshi, Gwamna Abba Kabir ya taya dukkan jama’ar jihar Kano murnar shiga sabuwar shekarar lafiya.
Abba ya ce ya na da tabbacin cewa sabuwar shekarar da za a shiga za ta zamo shekarar samun ci gaba ga jihar Kano.
Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin tabbatr da bukatun al’umma sun samu kulawa don samar da ci gaba a jihar.
Ya ce: “Ina taya al’ummar jihar Kano murnar wannan rana, ina da tabbacin sabuwar shekarar za ta kawo ci gaban da ba a taba gani ba ga al’ummar jihar.
Gwamnatina za ta ci gaba da kula da bukatun al’umma don samar da ci gaba a bangarori da dama a jihar.”
Ya ce tabbas an samu matsaloli da dama a shekarar da ta gabata inda ya ce sabuwar shekarar za ta zo da ci gaba.
Ya ce: “Ina cikin farin ciki da tura gaisuwa ga ‘yan Najeriya gida da waje kan murnar shiga sabuwar shekara.
“Tabbas shekarar da ta wuce an samu matsaloli a kasar baki daya, kuma ina fatan sabuwar shekarar za ta zo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
From ISYAKU.COM